logo

HAUSA

Kasar Sin tana sahun gaba a duniya wajen kera jiragen ruwa a fannoni 3

2022-01-17 14:01:56 CRI

Jiya Lahadi, kungiyar masana’antar kera jirgin ruwa ta kasar Sin ta fitar da alkaluman dangane da wannan sha’ani na shekarar 2021, inda aka nuna cewa, fannoni 3 dake shafar wannan sha’ani wato yawan jiragen ruwa da aka samar, da yawan karin da sabbin takardun oda da ake da su dukkansu sun kai kashi 50% na duk duniya, hakan ya sa kasar Sin yake ci gaba da kasancewa a sahun gaba a duniya.

A shekarar 2021, kamfanonin kera jiragen ruwa guda 6 na Sin suna cikin fitattun kamfanoni 10 a duniya a wadannan fannoni 3. Daga cikinsu, a karo na farko ne kamfanin kera jiragen ruwa na kasar Sin ya zarce kamfanin Hyundaiheavy na Korea ta kudu, inda ya zama kamfanin kera jiragen ruwa mafi girma a duniya, wanda ya samar da jiragen ruwa 206 a cikin shekarar 2021, alkaluman da ya kai kashi 20.2% bisa dukkan jiragen ruwa da aka kera a duk duniya. Kana darajar kwangilar oda da ya samu, ta kai fiye da kudin Sin RMB biliyan 130, inda ya karya lambun bajimta da ya kafa a shekarar 2008. (Amina Xu)