logo

HAUSA

Yawan al'ummar kasar Sin ya ci gaba da karuwa a shekarar 2021

2022-01-17 14:52:24 CRI

Yawan al'ummar kasar Sin ya ci gaba da karuwa a shekarar 2021_fororder_220117-Ibrahm-Populatioan

Alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta fitar Litinin din nan sun nuna cewa, yawan al'ummar kasar dake babban yankin kasar, ya karu zuwa biliyan 1.4126 a karshen shekarar da ta gabata.

Bayanai daga ofishin kididdigar kasar sun nuna cewa, alkaluman yawan jama’a na baya-bayan nan, sun karu da 480,000, idan aka kwatanta da karshen shekarar 2020.

Adadin sabbin haihuwa a shekarar 2021 ya kai miliyan 10.62. (Ibrahim)