logo

HAUSA

Tsohon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya mutu

2022-01-17 11:37:31 CRI

Tsohon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya mutu_fororder_220117-yaya 1-Kaita Mali

Allah ya yiwa tsohon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita rasuwa jiya Lahadi a Bamako, babban birnin kasar Mali, kamar yadda wata majiya ta kusa da iyalansa suka bayyana a babban birnin kasar jiya Lahadi. Ya rasu yana da shekaru 76.

Har yanzu dai ba a san musabbabin mutuwar tasa ba.

Marigayin ya hau karagar mulkin ksar Mali ce a watan Satumban 2013, aka kuma sake zabensa a shekarar 2018. Kwamitin ceton jama'ar kasar (CNSP) ya hambarar da Keita a ranar 18 ga watan Agustan shekarar 2020, bayan watanni jama’a na zanga-zanga a kan titunan kasar, inda suke kalubalantar gwamnatinsa.

Jim kadan bayan juyin mulkin da ya hambarar da shi, gwamnatin mulkin sojan kasar ta ba shi dukkan wasu hakkoki a matsayinsa na tsohon shugaban kasar Mali.

Bayan hambarar da shi ne kuma, ya sha zama a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, saboda rashin lafiya. (Ibrahim Yaya)