logo

HAUSA

Shugaban Gabon ya nuna yabo kan makarantar da kamfanin Sin ya gina a Libreville

2022-01-16 16:35:52 CRI

Shugaban Gabon ya nuna yabo kan makarantar da kamfanin Sin ya gina a Libreville_fororder_hoto2

A ranar 14 ga wata, shugaban kasar Gabon Ali-Ben Bongo Ondimba, ya kai ziyara a babbar makarantar Libreville, wadda kamfanin kasar Sin ta taimaka wajen ginawa a birnin Libreville, fadar mulkin kasar.

Fadin makarantar ya kai muraba’in mita dubu 17, ciki har da yankuna guda biyar, da suka hada da gidan renon kananan yara, da makarantar firamare, da kuma makarantar sakandare.

Shugaba Bongo ya ce, kamfanin kasar Sin ya gina wata babbar makaranta mai inganci, ya kuma kammala aikin gina makaranta kamar yadda aka tsara, lamarin da ya sa, za a iya bude makaranta bisa lokacin da aka tanada.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, kasar Gabon tana kokarin raya ayyukan ba da ilmi da kiwon lafiya, tana sa ran karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin kan wadannan fannoni. Kana, yana maraba da kamfanonin kasar Sin da su karbi ayyukan gine-gine da gwamnatin kasar Gabon ta zuba jari don ginawa, da ba da gudummawarsu wajen raya harkokin ba da ilmi da kiwon lafiya na kasar Gabon, ta yadda za a inganta bunkasuwar tattalin arzikin kasar Gabon, da kuma cimma moriyar juna.

Bayan aka fara amfani da babbar makarantar Libreville, a kowace shekara, za a sami dalibai sama da dubu 5 dake karatu a makarantar, lamarin da zai taka muhimmiyar rawa wajen raya harkokin ba da ilmi a kasar. (Maryam)