logo

HAUSA

Gwamnatin Zimbabwe ta ba da cikakken goyon baya ga gasar Olympics ta lokacin hunturu na Sin

2022-01-16 20:48:00 CRI

Gwamnatin Zimbabwe ta ba da cikakken goyon baya ga gasar Olympics ta lokacin hunturu na Sin_fororder_zimba

A bisa ga rahoton da jaridar Herald ta kasar Zimbabwe ta wallafa a ranar 15 ga watan Janairu ta bayyana cewa, ministar yada labaran kasar Zimbabwe, Monica Mutsvangwa, ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta ba da cikakken goyon bayanta ga gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing ta shekarar 2022, kana tana adawa da yunkurin siyasantar da gasar wasannin ta Olympics da wasu kasashe ke yi. Zimbabwe tana yiwa kasar Sin fatan samun cikakkiyar nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. (Ahmad)