logo

HAUSA

Mata ‘yan gudun hijira na Najeriya za su halarci gasar AFCON a Kamaru

2022-01-16 16:32:12 CRI

Mata ‘yan gudun hijira na Najeriya za su halarci gasar AFCON a Kamaru_fororder_UNHCR

Babban ofishin kula da ‘yan gudun hijira na MDD (UNHCR), ya sanar cewa, an bayar da damammakin da suka dace ga kungiyar wasan kwallon kafa ta dukkan mata wadda ta kumshi ‘yan gudun hijira 20 daga Najeriya inda za su halarci gasar ta neman cin kofin kasashen Afrika AFCON dake gudana a jamhuriyar Kamaru.

Yan gudun hijirar za su halarci gasa tsakanin kasarsu Najeriya da Sudan a Garoua, babban birnin shiyyar arewacin Kamaru a yau Asabar.

Kakakin hukumar ta UNHCR ya ce, an kwashe su daga sansanin ‘yan gudun hijira na Minawao dake yankin arewa mai nisa a Kamaru inda ake kula da dubban ‘yan gudun hijira daga Najeriya wadanda suka tserewa hare haren mayakan ‘yan ta’adda na Boko Haram.

Xavier Bourgois, kakakin hukumar UNHCR ya ce, hukumar ta yi cikakkiyar amanna na shigar da dukkan bangarori a wasanni. A sansanin ‘yan gudun hijira na Minawao, akwai matasa dake wasannin kwallon kafa kuma suna sha’awar nuna goyon bayansu ga kungiyar wasansu. Don haka ana fatan ba su damar ganawa da tawagar ‘yan wasan kasarsu.

Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar Mohammed Tchiroma ya ce, ya zo ne don nuna goyon baya ga kasarsa Najeriya. Ya ce a ko’ina yake a duniya ba zai taba mantawa da kasarsa ba.(Ahmad)