logo

HAUSA

Kamaru ta rage lokutan aiki da karatu don samun dandazon ‘yan kallon gasar AFCON

2022-01-16 15:39:55 CRI

Kamaru ta rage lokutan aiki da karatu don samun dandazon ‘yan kallon gasar AFCON_fororder_AFCON

Hukumomi a jamhuriyar Kamaru sun sanar a jiya Asabar cewa, za a rage yawan lokutan sa’o’in aiki da na karatun makarantu, da nufin kara yawan masu sha’awar kallon gasar wasannin cin kofin kasashen Afrika ta AFCON wanda kasar ta tsakiyar Afrika ke karbar bakuncinta.

Seraphin Magloire Fouda, babban sakatare a ofishin firaministan kasar, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, a kwanakin gudanar da wasannin na AFCON, makarantun kasar za su fara aiki ne daga karfe 7:30 na safe zuwa karfe 1:00 na rana. Kana ma’aikatan gwamnati za su fara aiki ne daga karfe 7:30 na safe zuwa karfe 2:00 na rana. A cewar sanarwar, gwamnati ta dauki wannan mataki ne da nufin baiwa al’ummar kasar Kamaru damar shiga a dama da su a wannan muhimmiyar gasar wasannin ta nahiyar Afrika.

Ya ce matakin zai fara ne daga ranar 7 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Fabrairu.

Gasar wasannin ta AFCON tana fuskantar karancin ‘yan kallo a filayen wasannin kasar, musamman a garuruwan Douala, Bafoussam da Limbe, inda ake gudanar da wasu daga cikin wasannin.

Hukumomin biranen kasar sun sanar a ranar Juma’a cewa, za su samar da motocin bus kyauta don daukar masu sha’awar kallon wasannin da mayar da su daga filayen wasannin.(Ahmad)