logo

HAUSA

Tsohon shugaban Najeriya ya bayyana baje kolin kasashen Afrika a matsayin hikimar bunkasa kasuwanci

2022-01-15 16:24:20 CMG

Tsohon shugaban Najeriya ya bayyana baje kolin kasashen Afrika a matsayin hikimar bunkasa kasuwanci_fororder_220115-Nijeriya-Ahmad

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa, baje-kolin dake gudana bayan shekaru biyu a tsakanin kasashen Afrika wato (IATF), wata muhimmiyar dama ce ta bunkasa cinikayya a tsakaninn kasashen nahiyar Afrika.

Obasanjo yayi wannan tsokaci ne a lokacin yin rajistar wa’adi na gaba na gudanar da bikin baje-kolin na IATF wanda aka tsara gudanarwa a Abidjan, babban birnin kasar Kwadebua a shekarar 2023, wanda sakateriyar yarjejeniyar kasuwanci maras shinge ta kasashen nahiyar Afrika (AfCFTA), da bankin shige da fice na Afrika suka gadanar.

Obasanjo wanda shine shugaban majalisar bada shawarwari na 2021 IATF yace, baje-kolin na IATF wani muhimmin ginshiki ne na kokarin da suke wajen gyara kura-kuran da suka faru a baya, da rusa shingayen kan iyakoki, da gina wasu gadoji da zasu taimaka wajen cimma burin ajandar samar da dawwamamman cigaban nahiyar nan da shekarar 2063, don gina Afrika irin wacce ake bukata.

Ya ce, ba kawai batu ne na baje-koli kadai ba, sai dai wani muhimmin shiri ne mai karfi na yin garambawul, kuma biki ne na bunkasa cigaban tattalin arziki wanda zai daga matsayin cigaban nahiyar Afrika ta hanyar kasuwanci, Obasanjo, wanda ya buga misali da baje-kolin 2021 IATF wanda ya gudana a birnn Durban, na kasar Afrika ta kudu.(Ahmad)

Ahmad