logo

HAUSA

Me ya sa kasar Sin ke dinga samun ci gaba a fannin ciniki?

2022-01-14 21:26:59 CMG

Me ya sa kasar Sin ke dinga samun ci gaba a fannin ciniki?_fororder_0114-ruiping-ciniki-Bello

Alkaluman da hukumar kwastam ta kasar Sin ta gabatar a yau Juma’a sun nuna cewa, yawan kudin cinikin shigi da fici da kasar Sin ta yi a bara ya kai dalar Amurka triliyan 6.05, wanda ya karya bajintar tarihi, da tabbatar da matsayin kasar na zama kan gaba a duniya a fannin cinikayya. Me ya sa kasar ke samun wannan nasara? Saboda kasar ta yi kokarin kare yaduwar cutar COVID-19 a cikin gida, kana ci gaban harkokin samar da kayayyaki da sayar da su su ma sun zama tushen karuwar tattalin arzikin kasar. Ban da wannan kuma farfadowar yanayin tattalin arzikin kasashe daban daban, da karuwar bukatun kayayyakin da ake samu a sauran kasashe, su ma sun taimakawa kasar Sin wajen samun ci gaban harkar ciniki. A wannan shekarar da muke ciki, kasar Sin na da cikakken imani kan ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kokarin raya bangaren ciniki na duniya, da taimakawa farfadowar tattalin arzikin kasashe daban daban. (Bello Wang)

Ibrahim