logo

HAUSA

Sin: Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing wani taron wasanni ne na zaman lafiya da hadin kai

2022-01-14 20:10:27 CMG

Sin: Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing wani taron wasanni ne na zaman lafiya da hadin kai_fororder_1

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a Jumma’ar nan cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, za ta sa kaimi ga hadin gwiwa tare da samar da fata ga daukacin bil-adama. Tana kuma fatan dukkan kasashe su yi biyayya ga kudurin ruhin Olympics.

Mai magana da yawun ma’aikatar Wang Wenbin, shi ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa, kan rahotannin shirin Amurka na shirya ayyukan horas da sojoji tare da kawayenta a yankunan da ke makwabtaka da kasar Sin a lokacin wasannin.

Ya zuwa yanzu, shugabannin kasashen duniya da dama sun bayyana fatansu da kuma goyon bayan gasar Olympics din dake tafe. Firayin ministan kasar Pakistan Imran Khan da babban sakataren MDD Antonio Guterres, duk sun sanar da cewa, za su halarci bikin bude gasar a nan birnin Beijing.(Ibrahim)

Ibrahim