logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da karuwar cin zarafin mazauna sansanin yan gudun hijira da ma’aikatan agaji a Syria

2022-01-14 11:03:20 CRI

MDD ta yi Allah wadai da karuwar cin zarafin mazauna sansanin yan gudun hijira da ma’aikatan agaji a Syria_fororder_220114-A2-Sham

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD ya yi Allah wadai da karuwar cin zarafi da kuma kisan kiyashin da ake yiwa ma’aikatan agaji a al-Hol, wani sansanin ’yan gudun hijira mafi girma a kasar Syria.

Kisa na baya bayan nan da aka samu shi ne na ranar Talata, wanda ya faru bayan wani harin da ’yan bindiga suka kaddamar kan asibitin dake sansanin, kamar yadda ofishin kula da ayyukan jin kai na MDDr (OCHA)  ya bayyana.

Wakilin MDD, kana jami’in kula da ayyukan jinkai na MDDr a kasar Syria, Imran Riza, da jami’in ayyukan jinkai na MDD na shiyyar mai kula da rikicin kasar Syria, Muhannad Hadi, sun yi Allah wadai da cin zarafin dake cigaba da faruwa a yankin.

OCHA ya sanar da cewa, mazauna sansanin ’yan gudun hijirar na al-Hol, suna bukatar mutuntuwa, da samar musu da dawwamamman tsarin magance matsalolin da suke fuskanta tun bayan da suka kauracewa gidajensu. Sannan MDD ta jaddada yin kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su dauki muhimman matakai na gaggawa don warware wadannan matsaloli, da kare hakkokin al’ummar, da kare mutuncinsu, da kuma martaba dukkan mazauna sansanin ’yan gudun hijirar na al-Hol. (Ahmad)