logo

HAUSA

Cikar gidan yarin Guantanamo shekaru 20 da kafuwa na nuna gazawar tsarin kare hakkin bil adama na Amurka

2022-01-14 10:57:37 CRI

Cikar gidan yarin Guantanamo shekaru 20 da kafuwa na nuna gazawar tsarin kare hakkin bil adama na Amurka_fororder_220114-S2-国际锐评-美式人权

Yayin da gidan yarin kare-kukan ka na Guantanamo ke cika shekaru 20 da kafuwa, sassan kasa da kasa na kara nuna rashin amincewa da tsare mutane a cikinsa. Masana na cewa har zuwa yanzu, Amurka ba ta dakatar da azabtar da fursunoni a gidan yarin ba, maimakon haka ma ta baza manufar amfani da irin wannan gidan yari a wasu karin sassan duniya.

Tun a shekarar 2005, jaridar “The Washington Post” ta Amurka ta bayyana cewa, hukumar leken asiri ta Amurka, CIA ta kafa wasu gidajen yari na sirri a nahiyoyin Asiya, ciki har da Thailand, da Afghanistan da wasu kasashen gabashin Turai.

Game da hakan, kafar Efe News ta bayyana cewa, wannan mataki na Amurka ya gurgunta daukacin tsarin kare hakkin bil adama na kasa da kasa. A cewar kafar, wadannan munanan gidajen yari sun zamo alamar zahiri, ta yadda Amurka ke take dokoki da ka’idojin kare hakkin bil adama. Kuma hakan na zama wani abun mamaki, ganin yadda ’yan siyasar Amurka ke kokarin tallata kwarewar kasar a fannin kare hakkin bil adama.

Ko shakka babu, matakan Amurka na cike da munafurci da yin baki biyu. Don haka abun da ya dace Amurka ta yi shi ne nazartar kanta, ta gaggauta rufe gidan yarin Guantanamo, da sauran makamantansa da aka kafa a asirce, kana ta gudanar da cikakken bincike da tabbatar da adalci. Lokaci ya yi da za a aiwatar da hakikanan matakai na kawo karshen wannan mummunan yanayi na take hakkin bil adama a tarihin wannan zamani.   (Saminu)