logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kwato mutane 26 daga hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna

2022-01-14 11:08:42 CRI

Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya Edward Gabkwet, ya ce wata rundanar musamman ta sojin sama, ta kwato mutane 26 daga hannun ’yan bindiga masu garkuwa da mutane, jim kadan bayan ’yan bindigar sun tusa keyar matafiya daga cikin wasu motocin sufuri zuwa cikin daji, a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Hare haren masu garkuwa da mutane dai na kara zama barazana ga sassan arewa maso yamma da yankin tsakiyar Najeriya, lamarin da kan haifar da kisa da kuma sace mutane. (Saminu)