logo

HAUSA

Afrika CDC: Kasashen Afrika sun yi gwajin COVID-19 sama da miliyan 91

2022-01-14 11:30:42 CRI

Afrika CDC: Kasashen Afrika sun yi gwajin COVID-19 sama da miliyan 91_fororder_220114-A3-AfricaCDC

Kasashen Afrika 53 sun yi gwajin cutar numfashi ta COVID-19 kimanin 91,331,072 ya zuwa yanzu, kamar yadda cibiyar dakile cutuka masu yaduwar ta Afrika CDC ta bayyana cikin bayananta na mako-mako wanda ta gabatar a baya bayan nan a ranar Talata.

Afrika CDC, kwararriyar hukumar lafiyar kungiyar tarayyar Afrika, ta bayyana cewa, an gudanar da sabbin gwaje-gwajen cutar kimanin 1,594,953 cikin mako guda da ya gabata.

Kasashe biyar da suka hada da Afrika ta kudu, Morocco, Tunisia, Libya da Habasha su ne ke da kusan kashi 62 bisa 100 na yawan adadin wadanda suka kamu da cutar a nahiyar Afrika.

A cewar hukumar, ya zuwa yammacin ranar Alhamis, adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai 10,173,541, kana cutar ta kashe mutane 232,562, yayin da mutane 9,061,284 sun warke daga cutar.

Afrika CDC ta ce, game da yawan adadin kamuwa da cutar, shiyyar kudancin Afrika ne annobar ta fi shafa, sai kuma yankin arewaci da gabashin Afrika dake bi mata baya, yayin da tsakiyar Afrika ne shiyya mafi karancin masu kamuwa da cutar a nahiyar. (Ahmad Fagam)