WHO na fatan sassan kasa da kasa za su kara maida hankali ga rigakafin COVID-19
2022-01-13 18:26:26 CRI
A Larabar makon nan, hukumar lafiya ta duniya WHO ta ja hankalin kasashen duniya game da yiwuwar ci gaba da bullar karin nau’o’in cutar COVID-19, tana mai fatan dukkanin sassa, za su rungumi matakan kandagarkin yaduwar cututtuka masu nasaba da numfashi, baya ga ita kanta cutar COVID-19.
A baya bayan nan dai, an samu karin sama da mutane miliyan 15 da suka harbu da cutar COVID-19 a sassan duniya daban daban cikin mako daya kacal, adadin da ya dara irin wanda aka taba samu a baya cikin mako guda. Masana sun alakanta hakan da saurin bazuwar da nau’in Omicron dake gaggauta maye gurbin nau’in Delta a kusan dukkanin kasashen duniya yake yi. Akwai kuma tsoron ganin karin fadadar wadannan alkaluma, yayin da ake dada fuskantar yanayin hunturu a wasu kasashe.
Duk dai da wadannan kalubale, masana kiwon lafiya na ganin adadin masu harbuwa da wannan annoba, ya fi yawa tsakanin rukunin al’ummun da ba su yi rigakafi ba, yayin da rigakafin ke dakile adadin wadanda cutar ke kwantarwa a asibitoci ko ma hallakawa.
Ko shakka babu, kiran da WHO ta yi, cewa a kara azama wajen tabbatar da nasarar alluran rigakafin cutar COVID-19 yana da ma’anar gaske, duba da yadda jinyar masu harbuwa da annobar ke dora wahalhalu masu tarin yawa, kan tsarin kiwon lafiyar kasashe daban daban.
Saboda haka, abu ne mai muhimmanci, kasashen duniya su kara hada karfi da karfe, wajen fadada samar da rigakafin COVID-19 a dukkanin sassan duniya, karkashin shirye shiryen kasa da kasa, kamar shirin nan na COVAX, musamman ga yankunan da aka fi tsananin bukatar su ba, tare da nuna banbanci ba.