logo

HAUSA

Soufianou Boubacar Moumouni: Ina kira ga matasan Nijar su tashi tsaye don rungumar karatu

2022-01-13 16:59:41 CRI

Soufianou Boubacar Moumouni: Ina kira ga matasan Nijar su tashi tsaye don rungumi karatu_fororder_微信图片_20220113164829

Kwanan nan ne Murtala Zhang ya zanta da wani matashi dan asalin birnin Yamai dake Jamhuriyar Nijar mai suna Soufianou Boubacar Moumoumi, wanda a yanzu haka yake karatu a fannin kimiyyar man fetur a jami’ar koyon ilimin man fetur ta kasar Sin dake Beijing.

Soufianou ya zo kasar Sin karatu tun shekara ta 2019. A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Soufianou ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin Nijar da kasar Sin, da matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka domin dakile yaduwar cutar COVID-19. A karshe ya bayyana fatansa ga matasan kasarsa wato Nijar. (Murtala Zhang)