logo

HAUSA

Kungiyar wasan kwallon curling ta kasar Kenya tana kokarin cimma burinta a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu

2022-01-13 19:15:32 CRI

Kungiyar wasan kwallon curling ta kasar Kenya tana kokarin cimma burinta a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu_fororder_Kenya

Kasar Kenya tana a yankin kusa da layin Equator, yanki ne mai zafi a duniya. Don haka, babu mutane da dama dake yin wasannin lokacin hunturu a kasar. A watan Oktoba na shekarar 2021, kasar Kenya ta kafa kungiyar wasan kwallon curling ta farko, inda a kan kira kungiyar da sunan kungiyar dake kunshe da ‘yan wasa mafi karancin shekaru a kasar. Koda yake ‘yan wasan kungiyar suna fuskantar kalubale da dama, kamar rufe wurin wasan kankara, da rashin samun kudin goyon bayan wasan da sauransu, amma kungiyar wasan kwallon curling ta kasar Kenya tana da burin shiga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing, wanda za a gudanar.

A kan kira wasan kwallon curling da sunan wasan chess a kan kankara, wasa ne dake bukatar da karfin jikin mutane, da kuma karfin kwakwalwa. Domin a kan yi wasan kwallon curling a cikin daki, an kuma samar da dama ga kasashen Afirka ta yin wasan, ta hakan an samar da dama ga ‘yan wasan Afirka wajen shiga wasannin Olympics na lokacin hunturu.

‘Yan wasan kungiyar wasan kwallon curling ta kasar Kenya, su kan yi wasan a kan kasa yayin horo. A watan Febrairu na shekarar 2021, kungiyar hadin gwiwa ta wasan kwallon curling ta kasar Kenya, ta shiga kungiyar hadin gwiwa ta wasan kwallon curling ta duniya, wadda ta zama mamba ta 67 a cikin kungiyar, kana ta zama kasa ta biyu daga nahiyar Afirka da ta shiga wasan kwallon curling a hukunce. A watan Oktoba na shekarar 2021, aka kafa kungiyar wasan kwallon curling ta kasar Kenya a hunkunce. Amma kungiyar ta fuskanci kalubale da dama game da samun horo. Shugabar kungiyar hadin gwiwa ta wasan kwallon curling ta kasar Kenya Lavender Oguta ta bayyana cewa,“Lokacin da na yi wasan kwallon rugby a kasar Ireland a shekarar 2015, na kalli gasar wasan kwallon curling a can, wannan ne karo na farko da na kalli gasar wasan kwallon curling, wasan ya ba ni sha’awa sosai. Amma a lokacin, ban taba tunanin zan iya yin wasan kwallon curling a kasar Kenya ba. A lokacin da aka kafa dakin kankara a kasar Kenya, sai na kafa ofishinmu don raya wasan. Amma a sakamakon tinkarar cutar COVID-19, an rufe dakin kankarar. Ba mu da sauran dakin yin wasan, kana ba mu da kayayyakin wasan don samun horo. Don haka, muna fuskantar kalubale da dama kan wannan batu.”

Don sa kaimi ga ‘yan wasa da su shiga wasan kwallon curling, gwamnatin kasar Kenya ta samar da dakin yin horo ga wasu kayan wasan ga kungiyar wasan kwallon curling ta kasar, kana an shirya gasar wasan a tsakanin kungiyar da kungiyar wasan ta kasar Denmark a kasar Kenya. Oguta ta ce, domin babu mai horaswa, ba kuma damar yin gasar wasan tare da sauran kungiyoyin wasan, ‘yan wasan kungiyar wasan kwallon curling ta kasar Kenya sun koyi fasahohi ta yanar gizo. Oguta ta ce,“Muna yin atisaye a kan kasa, muna kashe lokaci da dama wajen kallon gasannin wasan kwallon curling a kan internet. A halin yanzu, mun fara koyar da daliban makarantu fasahohin wasan, don samar da horo ga matasa, wadanda mai yiwuwa za su halarci gasar wasan ta matasa. Kana muna yin kokarin yin mu’amala tare da Sin, da Japan, da Amurka don neman hadin gwiwa tare da su, wajen raya wasan kwallon curling na kasar Kenya.”

Yawancin ‘yan wasan kungiyar wasan kwallon curling ta kasar Kenya, su fito ne daga kungiyar wasan kwallon rugby, da wasan kwallon kafa, wasan Kabaddi da sauransu, dukkansu suna da kwarewa kan wasannin motsa jiki. A ganinsu, idan sun zabi shiga wasan kwallon curling, zai ba su karin damar samun shiga gasar wasannin Olympics. Mercy Muasa tana daya daga cikinsu. Muasa ta bayyana cewa,“A lokacin da, ni dan wasan Kabaddi ne, amma na ji rauni. Ina sha’awar wasan kwallon curling, ina son yin wasan kwallon curling, a gani na, wannan wasa ya bani wata dama, ina bukatar da yin namijin kokari a wasan kwallon curling, domin wannan ne karo na farko da na yi wasan a matsayin memban kungiyar kasar Kenya. Mai yiwuwa ne zan samu damar shiga gasar wasannin Olympics, kowane dan wasa yana da burin shiga gasar wasannin Olympics.”

Ya zuwa yanzu, akwai membobi fiye da dubu daya a cikin kungiyar hadin gwiwa ta wasan kwallon curling ta kasar Kenya, shugabar kungiyar Oguta na ganin cewa, wannan babbar nasara ce, domin hakan zai sa kaimi ga karin kasashen Afirka, su fara maida hankali ga shiga wasan kwallon curling. Watakila wadannan sabbin kungiyoyin kasashen Afirka ba za su iya samun damar halartar gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da za a gudanar a birnin Beijing a wannan shekara ba, amma a nan gaba za su samu damar yin takara da halartar gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu mai zuwa. Oguta ta bayyana cewa,“A nan ina fatan dukkan kungiyoyin wasan kwallon curling masu halartar gasar wasannin Olympics ta birnin Beijing, za su samu sakamako mai kyau. Muna nuna goyon baya gare su. Za mu kalli gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ta talabijin ko yanar gizo.” (Zainab)