logo

HAUSA

Masanin Tanzania: Sin ta share fagen cigaban kasashe masu tasowa

2022-01-12 16:06:51 CRI

Masanin Tanzania: Sin ta share fagen cigaban kasashe masu tasowa_fororder_20220112-坦桑尼亚莫西教授

Farfesa Humphrey Moshi, daraktan cibiyar nazarin al’amurran kasar Sin a jami’ar Dar es Salaam ta kasar Tanzania, ya bayyana a tattaunawarsa da rukunin kafafen yada labaran kasar Sin CMG cewa, cigaban da kasar Sin ta samu cikin gomman shekarun da suka gabata ya kafa babban tarihin da ba a taba ganin irinsa ba ta fuskar sauri da kuma shigar da dukkan bangarori. Salon ci gaban kasar Sin ya samar da sabbin damammakin ci gaban kasashe masu tasowa.

Farfesa Mossi ya bayyana cewa, dandalin FOCAC ya kafa tarihi wajen cimma manyan nasarorin bunkasa ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma tun bayan kafa shi. Sabbin tsare-tsare da kudurori da aka gabatar a taron ministoci karo na 8 na FOCAC, ba kawai za su karfafa hadin gwiwar Sin da Afrika ba ne, har ma za su daga matsayin ci gaban tattalin arziki da yanayin zaman rayuwa a nahiyar Afrika. (Ahmad)