Biyan kudin diyya ga fursunan gidan yarin sirri na Amurka a ketare ba zai boye mumunan yanayin hakkin dan adam da take ciki ba
2022-01-12 10:13:10 CRI
A kwanakin baya bayan nan, Abu Zubaydah, wanda ake kiran shi “fursunan rai da rai”, wato ba za a sake shi daga gidan yari ba, ya sake jawo hankalin al’ummun kasa da kasa.
Kotun hakkin dan adam ta Turai ta yanke hukunci a shekarar 2018 cewa, gwamnatin Lithuania, ta yarda hukumar CIA ta Amurka ta daure Zubaydah cikin kurkukun sirri a kasar, lamarin ya sabawa dokar Turai, don haka ta bukaci gwamnatin Lithuania ta biya kudin diyya har Euro dubu 100 gare shi. Yanzu haka, wato bayan shekaru uku da suka gabata, gwamnatin Lithuania ta sanar da cewa, ta biya kudin diyyar.
Lamarin ya nuna cewa, gwamnatin Lithuania ta amince da matakin da ta dauka na take hakkin dan adam. Kaza lika ta amince da cewa, akwai kurkukun sirrin Amurka a kasarta.
A cikin shekaru 20 da suka gabata, an daure Zubaydah a cikin kurkukun sirri da hukumar CIA ta kafa a ketare, inda aka rika cin zalin sa matuka, kuma ko kadan, Amurka ba ta samar da shaidun alakarsa da kungiyar Al Qaeda ba, kana ba ta gabatar da kara a kan sa ba.
A bayyane take cewa, kudin diyyar da aka biya shi, bai iya boye mumunan yanayin hakkin dan adam da Amurka ke ciki ba. Jaridar New York Times ita ma ta yi nuni da cewa, tayar da yake-yake, da daukar matakan da ba su dace ba kamar yadda take so a fadin duniya, sun riga sun sa kasar ta Amurka ta rasa kwarjinin da’a daga duk fannoni a idon al’ummun kasa da kasa. (Jamila)