logo

HAUSA

Tsarin amfani da na’urorin zamani na aiki yadda ya kamata gabanin bude gasar Olympics ta birnin Beijing

2022-01-12 10:47:03 CRI

Tsarin amfani da na’urorin zamani na aiki yadda ya kamata gabanin bude gasar Olympics ta birnin Beijing_fororder_20220112-Beijing Olimpics-Saminu2

Mashirya gasar wasanni Olympics ta lokacin hunturu dake tafe nan da ’yan kwanaki a birnin Beijing, da ajin gasar na nakasassu, sun bayyana cewa, tsarin gwaji na amfani da na’urorin zamani domin tabbatar da gudanar gasar cikin nasara, ba tare da wani tsaiko ba, na tafiya yadda ya kamata.

An kaddamar da tsarin na gwaji ne a ranar 4 ga watan Janairun bana, kuma tuni kusan ’yan jaridu da masu watsa shirye shirye 1,500 daga sassan duniya daban daban suka iso birnin na Beijing.

Kakakin kwamitin shirya gasar ta Olympics ta birnin Beijing ko BOCOG a takaice, Mr. Zhao Weidong ya ce, an kammala dukkanin tsare-tsaren gasar ta bana a kan lokaci, kuma tsare-tsaren sun kai matsayin koli a inganci, kasancewar an yi hadin gwiwa da tattaunawa da abokan hulda na sassan kasa da kasa.

A wani ci gaban kuma, kwamitin BOCOG ya kira taron manema labarai a jiya Talata ta kafar bidiyo, domin kaucewa haduwar mutane a wuri guda, tare da tabbatar da halartar dukkanin sassa.

Kamar dai yadda aka bayyana cikin kundin shirye shiryen gasar ta bana, ana bukatar tsarin amfani da na’urorin zamani, domin tabbatar da gudanar gasar cikin matakan kare lafiyar dukkanin mahalartan ta.

Daraktan sashen watsa labarai na kwamitin BOCOG Xu Jicheng, ya ce za a ci gaba da gwajin da aka fara tun daga ranar 4 zuwa 22 ga watan nan na Janairu. Kimanin ’yan jarida 10,000, da masu watsa shirye shirye da dama ne ake sa ran za su gudanar da ayyuka a yayin gasar, kuma BOCOG zai samar da hidimomi na zamani domin su, bisa tsarin da aka amincewa tare da biranen da za su karbi bakuncin gasar    (Saminu)