logo

HAUSA

Tsohon shugaban rikon kwarya na Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

2022-01-12 11:23:27 CRI

Tsohon shugaban rikon kwarya na Najeriya Ernest Shonekan ya rasu_fororder_20220122-Sernest-shonekan

Tsohon shugaban rikon kwarya na tarayyar Najeriya Ernest Shonekan ya rasu a jiya Talata a Lagos, yana da shekaru 85 a duniya. An hambarar da gwamnatin da Shonekan ya jagoranta ne, yayin juyin mulkin sojin watan Nuwamba na shekarar 1993.

Cikin wata sanarwar da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar, shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari, ya gabatar da sakon ta’aziyyar rasuwar Shonekan, yana mai bayyana mamacin a matsayin mutum mai matukar kaunar zaman lafiya, da aiki tukuru, wanda ya ba da gudummawa matuka ga ci gaban mulkin dimokaradiyyar kasar.

An haifi marigayi Shonekan ne a birnin Lagos, a watan Mayun shekarar 1936. Ya kuma mulki Najeriya a matsayi na rikon kwarya daga ranar 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwambar shekarar 1993, inda ya maye gurbin gwamnatin soji ta Janar Ibrahim Babangida. Daga baya kuma Janar Sani Abacha ya hambarar da gwamnatin na Shonekan. (Saminu)