logo

HAUSA

Shugaban Najeriya Ya Musanta Jita-Jita Da Ake Yadawa Wai Rancen Kudin Da Sin ke bin Kasar Tarko Ne

2022-01-12 15:48:10 CRI

Shugaban Najeriya Ya Musanta Jita-Jita Da Ake Yadawa Wai Rancen Kudin Da Sin ke bin Kasar Tarko Ne_fororder_src=http___p3crires.cri.cn/yafei/p2_M00_A4_DC_CqgNOlh2022AQ6IHAAAAAAAAAAA357.600x401&refer=http___p2.cri

Daga Amina Xu

Abokaina, shin a ra’ayinku rancen kudin da Sin ke baiwa Najeriya tarko ne ko taimako mai kyau? Ga amsar da shugaban Najeriyar Muhmamadu Buhari ya bayar. Kwanan baya, lokacin da shugaban ya amsa tambayoyin da aka yi masa game da wannan batu da kuma bunkasuwar manyan ababen more rayuwar kasar, ya bayyana cewa, kasarsa ta nemi rancen kudi ne bisa bukatunta. Ya ba da misali da yanayin zirga-zirga daga Lagas zuwa Ibadan, inda kasar Sin ta taimaka wajen gina layin dogo da hanyar mota tsakanin wadannan birane biyu, don haka, me ya sa kasar za ta ki karbar rancen kudi daga Sin? Idan ta yi watsi da shi, to jama’ar biranen biyu ba za su samu saukin zirga-zirga tsakanin wadannan birane ba. Shugaban ya ce, kasar Najeriya na maraba da dukkan masu sha’awar taimaka mata wajen bunkasa hanyoyin mota da layin dogo da na’urorin samar da wutar lantarki.

Shugaban Najeriya Ya Musanta Jita-Jita Da Ake Yadawa Wai Rancen Kudin Da Sin ke bin Kasar Tarko Ne_fororder_80f52e5e09a04aca9be009b466d5ac8c

Shugaba Muhmamadu Buhari ya bayyana matsayinsa game da rancen kudi da kasar Sin ke binta, da yadda kasar ta yi amfani da su wajen kyautata zaman rayuwar jama’a da raya tattalin arziki, kuma kasarsa na maraba da duk wani taimako daga kasashen waje. Amma, me yasa kasar ta fi samun rancen kudi daga kasar Sin a maimakon wasu kasashen yamma?

Dalili kuwa shi ne kasashen yamma na matukar son kare moriyarsu ne kawai, amma Sin ta dauki matsayin samun moriya tare. Rancen kudin da Sin take baiwa kasashe masu tasowa musamman ma kasashen Afrika, bashi ne mai saukin biya, wasu har ma babu ruwa a cikinsu. Alal misali, rancen kudin da Najeriya ta karba daga kasar Sin, kudin ruwa ya kai kashi 2.8% ne kawai, kuma za ta iya biya cikin shekaru 20 masu zuwa. Babu kasashen yamma da za ta iya samar da rancen kudi bisa wannan gatanci. Kasashen Afrika suna yin amfani da kaso 40 cikin 100 na rancen kudin da suka samu daga kasar Sin wajen samar da wutar lantarki, saura 30% kuma ake yin amfani da su wajen kyautata manyan ababen more rayuwa na zirga-zirga. Wannan ya nuna cewa, kasar Sin ce kadai, za ta iya daukar irin wannan mataki wanda da kyar za ta samu riba mai yawa a cikinsa, saboda a ganinta kasashen Afrika kawayenta ne da ya kamata su yi hadin kai don samun bunkasuwa da cin moriya tare, amma kasashen yamma ba su da wannan manufa ko kadan. Hakan ya sa shugaba Buhari ya amince da rancen kudin da Sin ta samar.

Saboda yadda hadin kan Sin da Afrika ke samun ci gaba mai armashi, ya sa kasashen yamma ke neman bata wannan alaka mai kyau. Kuma bunkasuwar kasashe masu tasowa cikin hadin kai, na kalubalantar babakaren kasashen yamma, idan kowa da kowa ya samu bunkasuwar tattalin arziki da jituwar al’umma, to yaya kasashen yamma za su iya yin shisshigi a harkokin sauran kasashe?, yaya za su kakabawa sauran kasashe takunkumi na tattalin arizki da kimiya babu gaira babu dalili? Hakan ya sa suke ta baza jita-jita da neman shafawa sauran kasashen bakin fenti a wannan fanni ta hanyar nuna fin karfinsu ta fuskar yada labarai a duniya.

Shafawa hadin kan Sin da Afrika kashin kaza, ya fusata kasashen Afrika, wannan ya sa shugaban Najeriya ya fito fili, inda ya musanta irin wannan jita-jita, saboda hadin kan kasar da Sin ya kawo moriya mai yakini ga Najeriya. Wasu kasashen yamma ba su kawo amfani ga jama’ar kasashen Afrika ba, kuma su ma kasashen Afrika suna sane da haka, shi ya sa suke kokari kare hadin kan bangarorin biyu. A ra’ayina, ya fi kyau wadannan kasashen yamma su yi watsi da ra’ayin babakare da neman shafa wa alakar Sin da kasashen Afirka bakin fenti, su ci gaba da yin hadin kai da samun moriya tsakanin jama’ar Afrika da Sin, su kuma amince da kasancewar bangarori daban-daban na duniya, saboda samun bunkasuwa tare ya dace da moriyar Bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)