logo

HAUSA

Wang Yi: kasar Sin na nuna goyon bayan neman ci gaban kasashen Afirka

2022-01-12 10:26:21 CRI

Daga Janairu 4 zuwa 7 ga watan Janairun shekarar 2022 ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ziyarci kasashe uku na nahiyar bisa gayyatar da aka yi masa, wato Eritrea da Kenya, da Comoros, domin kiyaye al'adar fara ziyartar kasashen nahiyar Afirka a farkon kowace shekara na kusan tsawon shekaru 32.

Wang Yi: kasar Sin na nuna goyon bayan neman ci gaban kasashen Afirka_fororder_220112世界22002-hoto3

A dukkan kasashen da Wang Yi ya ziyarta, ya bayyana adawar kasarsa ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe da aniyar kasar Sin ta taimakawa kaashen nahiyar wajen yaki da annobar COVID-19 da aiwatar da sakamakon da aka cimma a yayin taron dandalin FOCAC.

Bugu da kari, Wang Yi ya jaddada manufar kasar Sin ta goyi bayan kasashen a fannin kare cikakken ’yanci, da yankuna da kuma martaba kimarsu, tare da adawa da sanyawa kasashen takunkumi babu gaira babu dalili.

Wang Yi: kasar Sin na nuna goyon bayan neman ci gaban kasashen Afirka_fororder_220112世界22002-hoto2

Ko shakka babu, wadannan kalamai na Mr. Wang, sun kara yin nuni ga jajircewar kasar Sin, wajen tabbatar da goyon bayanta ga kawayenta na Afirka a dukkanin fannonin ci gaban su.

Wadannan dalilai ne kuma, suka sanya dukkanin masu kishin ci gaban Afirka, ke ganin a yanzu da ma nan gaba, kasashen nahiyar na da tarin alfanu da za su ci gaba da samu, karkashin wannan dangantaka mai dogon tarihi.

Wang Yi: kasar Sin na nuna goyon bayan neman ci gaban kasashen Afirka_fororder_220112世界22002-hoto4

Game da zargin da ake yiwa Sin, na danawa kasashen Afirka tarkon bashi kuwa, Wang ya ce Sin da nahiyar Afirka na gudanar da hadin gwiwa yadda ya kamata, an kuma kirkiri batun tarkon bashi ne domin jefa kasashen nahiyar cikin shakku, ta yadda za su dawwama cikin talauci da koma baya.

Don haka a cewarsa, Sin za ta ci gaba da aiki tare da kasashen Afirka, wajen zartas da manufofin inganta rayuwar al’umma, tare da ba da karin gudummawa ga sashen bunkasawa, da zamanantar da masana’antun nahiyar. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)