logo

HAUSA

CMG ya yada wasannin Olympics na Beijing ga masu sha’awar wasan kankara na Amurka

2022-01-12 13:24:45 CRI

A ranar 10 ga wata, agogon Amurka, babbar tashar ‘yan jaridu ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, dake nahiyar arewancin nahiyar Amurka, ya shirya wani biki mai taken “Bari mu more makoma tare yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Beijing”, a dakin wasannin motsa jiki na Washington, fadar mulkin kasar Amurka, inda aka yada wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing dake tafe, ga ‘yan kallon nahiyar a zihiri, da kuma ta kafar yanar gizo.

CMG ya yada wasannin Olympics na Beijing ga masu sha’awar wasan kankara na Amurka_fororder_a

Yayin nuna bikin, mataimakin ministan ma’aikatar yada manufofi ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaba kana babban edita na CMG Shen Haixiong, da jakadan kasar Sin dake Amurka Qin Gang, sun gayyaci masu sha’awar wasan kankara na Amurka, da su kalli gasannin da za a yi yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, tare kuma da taya su murnar zuwan shekarar damisa, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ta kafar bidiyo.

CMG ya yada wasannin Olympics na Beijing ga masu sha’awar wasan kankara na Amurka_fororder_b

Shen Haixiong ya bayyana cewa, CMG ya kafa taragun watsa shirye-shiryen talabijin kai tsaye da fasahar 5G na farko a duniya, a kan hanyar dogo zuwa filin gasa na wasannin, inda za a gayyaci ‘yan jaridun kasa da kasa su yi amfani da taragun tare yayin gasa, ta yadda za a samar da wani gaggarumin taron wasannin Olympics ga masu kallo na duk duniya.

CMG ya yada wasannin Olympics na Beijing ga masu sha’awar wasan kankara na Amurka_fororder_c

Yan wasan kasar Sin da Amurka, wadanda ke share fage domin shiga gasar, da sauran mutane na fannoni daban daban su ma na fatan za a gudanar da gasar cikin nasara.  (Jamila)