logo

HAUSA

An bukaci al’ummun gabashin Afrika su yi fitar farin dango don karbar riga-kafin COVID-19

2022-01-12 10:52:55 CRI

An bukaci al’ummun gabashin Afrika su yi fitar farin dango don karbar riga-kafin COVID-19_fororder_20220112-EAC-Ahmad2

Kungiyar raya yankin gabashin Afrika (EAC) ta bukaci al’ummun shiyyar gabashin Afrika da su fita kwansu da kwarkwata domin karbar riga-kafin cutar numfashi ta COVID-19 a matsayin muhimmin komari na bai daya don dakile yaduwar annobar a shiyyar.

Peter Mathuki, sakatare-janar na kungiyar EAC ya karfafa gwiwar mutanen da suka kammala karbar riga-kafin da su sake karbar nau’in riga-kafin mai karfafa garkuwar jiki domin ci gaba da samun kariya daga annobar.

Mathuki ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, kin amincewar karbar riga-kafin yana mayar da hannu agogo baya a kokarin da ake na farfadowar tattalin arzikin shiyyar bayan komadar da ya samu a sanadiyyar barkewar annobar. Ya ce bisa tsarin da duniya ke tafiya kansa a halin yanzu shi ne nan gaba masu tafiye tafiye da kuma masu son halartar tarukan kasa da kasa za a bukace su gabatar da shaidar karbar riga-kafin.

Mambobin kasashen EAC su ne Burundi, Kenya, Rwanda, Sudan ta kudu, Tanzania da Uganda. Kuma helkwatar EAC tana birnin Arusha, na kasar Tanzania. (Ahmad)