logo

HAUSA

Iran ta yaba da yadda zagaye na 8 na tattaunawar Vienna ke gudana

2022-01-12 14:33:13 CRI

Iran ta yaba da yadda zagaye na 8 na tattaunawar Vienna ke gudana_fororder_20220112-Iran-Saminu4

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian, ya ce ya gamsu da yadda zagaye na 8 na tattaunawar da ake yi a Vienna game da batun nukiliyar Iran ke gudana. 

Abdollahian, wanda ya yi tsokacin a jiya Talata, ya ce shawarwarin da ake yi game da lalubo hanyoyin farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar sa ta shekarar 2015 a wannan karo, sun dara sauran da aka yi a baya armashi. Ya ce ya zama wajibi a jinjinawa shawarwarin da Iran ta gabatar, domin sun taimaka wajen cimma nasarorin da aka samu.

Ministan ya kara da cewa, domin kammala yarjejeniyar, dole ne daukacin sassa masu ruwa da tsaki, su cika alkawuran su karkashin yarjejeniyar. Ko da yake a cewar sa, har yanzu Iran ba ta ga alamun himma daga Amurka, da sauran kasashe 3 daga Turai a wannan fanni ba.    (Saminu)