logo

HAUSA

CAF: ‘Yan sandan Kamaru na gudanar da bincike game da cin zarafin wasu ‘yan jaridar Aljeriya a Douala

2022-01-11 09:55:48 CRI

Hukumar gudanarwar kwallon kafar nahiyar Afirka CAF, ta ce ‘yan sandan kasar Kamaru na gudanar da bincike, game da yadda wasu bata gari suka yiwa wasu ‘yan jaridar kasar Aljeriya fashi, lokacin da suke fitowa daga otal din su, inda suka kwace musu kayayyaki da fasfo, tare da raunata 2 daga cikin su.

Cikin wata sanarwa, CAF ta ce ‘yan jaridar sun gabatar da korafi, game da yadda aka ci zarafin su a birnin Douala, daya daga garuruwan da a yanzu haka ke karbar bakuncin wasannin gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka.

Kaza lika, sanarwar ta ce CAF na hadin gwiwa da mahukuntan birnin na Douala, domin tantance hakikanin halin da ake ciki, kana hukumar ta zanta da ‘yan jaridar, ta kuma yi musu fatan samun sauki cikin sauri, tana mai cewa, kare lafiya da dukiyoyin masu halartar gasar ta AFCON dake gudana a Kamaru, na cikin manyan burikan CAF da sauran abokan huldar ta.  (Saminu)