logo

HAUSA

Sojoji sun hallaka ‘yan bindiga 5 a jihar Kaduna

2022-01-11 09:11:29 CRI

Sojoji a Najeriya sun hallaka ‘yan bindiga 5, a kusa da garin Kwanan Bataro dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a jiya Litinin, inda ya ce sojoji sun samu wasu bayanan sirri, na zirga zirgar ‘yan bindigar, kuma nan take suka kai musu farmaki tare da hallaka 5 daga cikin su.

Ana dai fuskantar hare haren masu garkuwa da mutane a arewacin Najeriya cikin watannin baya bayan nan, lamarin da kan sabbaba hallaka mutane da sace wasu.  (Saminu)