logo

HAUSA

Lawal Saleh: Ziyarar Wang Yi a Afirka a farkon bana na da babbar ma’ana

2022-01-11 15:45:12 CRI

Lawal Saleh: Ziyarar Wang Yi a Afirka a farkon bana na da babbar ma’ana_fororder_微信图片_20220110145243

Daga ranar 4 zuwa 7 ga wata, memban majalisar gudanarwa ta kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kai ziyara wasu kasashen Afirka uku, da suka hada da Eritrea, Kenya da kuma Comoros. Ziyarar da kowane ministan harkokin wajen kasar Sin ke kaiwa sassan nahiyar Afirka, a farkon duk shekara cikin shekaru 32 kawo yanzu. Al’amarin da ya dada nuna irin muhimmanci da Sin ke dorawa ga sha’anin raya dangantakar sassan biyu.

Game da ziyarar Wang Yi a wannan karo, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da Lawal Saleh, wani shahararren mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, kana masanin harkokin kasashen waje dake birnin Abuja na tarayyar Najeriya.

Malam Lawal Saleh ya bayyana ra’ayinsa kan ma’anar ziyarar minista Wang ga nahiyar Afirka, da yadda al’ummomin Afirka za su samu alfanu daga dangantakar Sin da Afirka karkashin dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC da kuma shawarar “ziri daya da hanya daya”, musamman a lokacin da duniya take fuskantar yaduwar annobar COVID-19 da sauran wasu manyan sauye-sauye. (Murtala Zhang)