logo

HAUSA

Ranar ’Yan Sandan Kasar Sin: Yabon Gwani ya Zama Dole

2022-01-11 14:33:05 CRI

Ranar ’Yan Sandan Kasar Sin: Yabon Gwani ya Zama Dole_fororder_0111-1

A jiya 10 ga wata ne, aka yi bikin ranar tunawa da ’yan sandan kasar Sin. A shekarar 2020 ne kasar ta ayyana 10 ga watan Junairun kowacce shekara, a matsayin ranar ’yan sanda, domin jinjinawa irin gudunmawar da ’yan sanda ke bayarwa ga tsaron alumma.

kamar yadda abinci da lafiya ke da muhimmanci ga bil adama, haka ma tsaro yake. kowacce alumma a duniya na muradin samun tsaron lafiya da dukiyoyi da kwanciyar hankalinta. Kana babu wata alumma, ko wata kasa da za ta samu ci gaba ba tare da samun ingantaccen tsaro ba. Sai dai duk da muhimmancinsa, akasarin alumma na mantawa da wadanda ke bada gagarumar gudunmawa wajen tabbatar musu da tsaro da kwanciyar hankali.

’Yan sandan kasar Sin sun kasance zarata, kuma masu aiki bisa kwarewa, lamarin da a ganina, shi ya kai kasar ga more irin kwanciyar hankali dake akwai. Zan iya cewa, daya daga cikin abubuwan da na fi alfahari da shi a zamana a kasar Sin shi ne: tsaro da kwanciyar hankali. Kuma wannan ya samo asali ne daga irin jajircewar ’yan sandan kasar wajen tabbatar da tsaro da doka. Hakika na zama shaida ga irin gudunmawar da suke bayarwa, haka kuma ko wanne mazaunin kasar, ciki har da baki, za su iya tabbatar da hakan. Asali ma, ranar ta 10 ga watan Janairu, ta samo asali ne daga lambar tuntubar ’yan sanda ta 110, domin samun taimakon gaggawa da aka kaddamar tun a ranar 10 ga watan Junairun shekarar 1986, wanda zuwa yanzu, bayan shekaru 30, ta zama alamar rundunar ’yan sandan kasar.

Lallai wadannan jamian tsaro da su ne mafi kusanci da alumma, sun cancanci yabo da girmamawa, domin tunawa da irin gudunmawarsu har da girmama su, zai kara musu kwarin gwiwa. Ya kamata a duk inda muke, mu rika tunawa cewa, su ma mutane ne kamar mu, kuma suna matukar bukatar goyon baya da fahimta da taimakonmu, domin saukaka aikinsu na ba mu kariya. Haka kuma, ya kamata kasashe da alummomi su yi koyi da wannan yunkuri na gwamnatin Sin na ware wata rana domin jinjinawa ’yan sanda, da wayar da kan alumma kan ayyukansu da muhimmancin ba su goyon baya.

Bisa kididdigar maaikatar kula da tsaron alumma ta kasar Sin, tun bayan kafuwar Jamhuriyar jamaar kasar a shekarar 1949 zuwa shekarar 2020, sama da jamian ’yan sanda 14,000 ne suka rasa rayukansu, yayin da sama da 100,000 suka jikkata. Sannan a rabin farko na shekarar 2020 kadai,  sama da ’yan sanda 169 sun mutu, a kokarinsu na yaki da annobar COVID-19 da kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiya.