logo

HAUSA

An yi bikin ranar rumfa kasar Sin a taron baje kolin Dubai na 2020

2022-01-11 11:18:46 CRI

An yi bikin ranar rumfa kasar Sin a taron baje kolin Dubai na 2020_fororder_220111-National Day of China Pavilion celebrated in Expo-Faeza3

An daga tutar kasar Sin da safiya jiya Litinin karkashin ginin alamar babban filin Al Wasl, inda ake gudanar da baje kolin birnin Dubai na 2020, lamarin da ke alamta fara bikin rumfar kasar.

Jakadan kasar Sin a Hadaddiyar Daular Larabawa, Ni Jian, da Ministan kula da dangantakar kasashen waje kuma manajan daraktan baje kolin na Dubai, Reem Ebrahim Al Hashimy, da mataimakin ministan harkokin waje da harkokin hadin gwiwa da ci gaban kasa da kasa, Sultan Mohamed Al Shamsi ne suka halarci bikin.

Jakadan kasar Sin Ni Jian, ya mika sakon taya murna daga mataimakin firaministan Sin, Hu Chunhua, wanda ya godewa kasar bisa irin taimakonta ga rumfar kasar Sin.

An yi bikin ranar rumfa kasar Sin a taron baje kolin Dubai na 2020_fororder_220111-National Day of China Pavilion celebrated in Expo-Faeza3-2

Da yake jinjinawa rumfar ta kasar Sin, Sultan Mohamed Al Shamsi, ya ce hadin gwiwa tsakanin kasarsa da Sin, ta kara karfi cikin shekarun da suka gabata, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, wadda kasar ke zaman muhimmiyar abokiyar hulda.

Yayin bikin mai taken “gina al’uma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama-kirkire kirkire da damarmaki” rumfar kasar Sin ta gabatar da sabbin nasarorin da kasar ta samu a bangarorin binciken sararin samaniya da fasahar sadarwa da fasahar AI, wadanda suka bude wata kafa ta hango kyakkyawar makomar bil adama. (Fa’iza Mustapha)