logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kai Nijeriya

2022-01-11 15:04:32 CRI

MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kai Nijeriya_fororder_古特雷斯

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da mummunan harin da aka kai jihar Zamfara dake arewa maso tsakiyar Nijeriya cikin karshen makon da ya gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.

Sakatare janar din ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rusta da su, tare da bukatar hukumomin Nijeriya su dauki dukkan matakan da suka dace na hukunta wadanda ke da alhakin kai harin.

Baya ga haka, ya tabbatar da goyon bayan majalisar ga yakin da Nijeriya ke yi da ta’addanci da rikice-rikice da manyan laifuffuka.

Tun daga karshen shekarar 2020, satar mutane don neman kudin fansa da sauran laifuffuka suka zama ruwan dare a arewa maso yammacin Nijeriya. (Fa’iza Mustapha)