logo

HAUSA

Fadar gwamnati: Al’amura sun daidaita a Kazakhstan

2022-01-10 11:07:35 CRI

Fadar gwamnati: Al’amura sun daidaita a Kazakhstan_fororder_220110-Saminu3

Fadar shugaban kasar Kazakhstan ta bayyana cewa, al’amura sun daidaita a dukkanin yankunan kasar, kuma yanzu haka al’ummar kasar na iya samun hidimomi daga ababen more rayuwa yadda ya kamata.

Wata sanarwa da ofishin watsa labarai na fadar shugaban kasar ya fitar a jiya Lahadi, ta ce yayin wani taro na tsara ayyuka da shugaba Kassym-Jomart Tokayev ya jagoranta, shugaban ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da dawo da doka da oda, da tsaro a sassan kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, a yanzu haka, an tsara gabatar da kara 125 gaban kuliya, yayin da tuni ’yan sanda ke tsare da mutane 5,800 da ake zargi da aikata laifuka, ciki har da ’yan kasashen waje da dama.

Tashin farashin mai ya harzuka al’ummar Kazakhstan, inda dubban ’yan kasar suka kwarara kan tituna tsawon kwanaki, sun yi zanga zangar nuna rashin amincewa da hakan, lamarin da ya haifar da rasuwar mutane da dama, baya ga wasu karin mutanen da suka jikkata, aka kuma lalata da kona wasu gine ginen gwamnati.

A yau Litinin ne kuma shugaba Tokayev ya ayyana makoki na kasa, domin jimamin wadanda suka rasu, sakamakon boren da ya gudana.  (Saminu)