logo

HAUSA

’Yan bindiga sun sako yara ’yan makaranta 30 a jihar Kebbi

2022-01-10 09:49:56 CRI

’Yan bindiga sun sako yara ’yan makaranta 30 a jihar Kebbi_fororder_220110-Saminu1-DalibanNijeriya

A Najeriya ’yan bindiga masu garkuwa da mutane, sun sako yara ’yan makarantar kwalejin gwamnatin tarayya ta Birnin Yauri dake jihar Kebbi su 30 tare da malamin su daya.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar ta Kebbi Yahaya Sarki ya fitar a jiya Lahadi, ta ce ’yan bindigar dake sace jama’a domin neman kudin fansa, sun sako yaran ne bayan tsare su tsawon sama da watanni 6.

Yahaya Sarki ya ce, tuni yaran da malamin su guda suka isa Birnin Kebbi, fadar mulkin jihar a ranar Asabar, ana kuma duba lafiyar su kafin hada su da iyalan su.

Tun a ranar 17 ga watan Yunin shekarar da ta gabata ne dai ’yan bindigar suka kai hari makarantar sakandare ta Birnin Yauri, suka kuma hallaka wani dan sanda daya, tare da yin awon gaba da dalibai masu tarin yawa.

Rahotanni sun ce kafin sakin daliban na wannan karo, ’yan bindigar sun rika sako wasu daga cikin daliban rukuni rukuni.

Ana dai yawan samun hare haren ’yan bindiga masu yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a yankunan arewacin Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a fadin nahiyar Afirka, inda bata garin kan hari makarantu tare da sace dalibai.  (Saminu Fagam)