logo

HAUSA

Sin Da Afirka: Muhimmancin Ziyarar Ministocin Harkokin Wajen Sin Zuwa Afirka Kowace Farkon Shekara

2022-01-10 16:17:38 CRI

Sin Da Afirka: Muhimmancin Ziyarar Ministocin Harkokin Wajen Sin Zuwa Afirka Kowace Farkon Shekara_fororder_src=http___images.haiwainet.cn_20200110_1578625463604196&refer=http___images.haiwainet

Daga: Lawal Sale

A kan wata kakkarfar al’ada da ta samo tushe shekarar 1991 (yau shekaru 32 da suka wuce), ministocin harkokin wajen kasar Sin suna ba nahiyar Afirka fifiko a ci gaba da kai ziyara ta farko a nahiyar a farkon kowace shekara.

Wannan al’ada dai tana nuna cewa kasar Sin da nahiyar Afirka tamkar tsintsiya ce mai madauri daya. Sassan biyu suna da daddadiyar dangantaka wacce a karkashinta suke taimakawa juna, da goyon bayan juna, da tsare mutuncin juna a ko da yaushe. Sassan biyu dai kasashe ne masu tasowa wadanda suna da abubuwa da yawa wadanda suka yi kammani.

A ci gaba da tsare al’ada, wannan karon a shekarar 2022 daga ranar 4 zuwa 7 na watan Janairu, mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyara kamar yadda aka saba zuwa kasashe uku wadanda suka hada da Eritrea da Kenya da Comoros. Wannan ziyara dai na nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora ga sha’anin raya dangantakar sassan biyu da kuma son ci gaban kasashen nahiyar Afirka a yanzu da nan gaba. A shekarar da ta gabata dai Minista Wang Yi ya ziyarci Najeriya, da Tanzaniya, da DR Kongo, da Botswana, da Seychelles.

A duk kasashe ukun da Minista Wang Yi ya kai ziyara a farkon wannan shekara, Minista Wang Yi ya jadadda manufar kasar Sin ta goyon bayan kasashen ta fannin kare ’yanci, da kuma martaba kimarsu tare da kauce tsoma baki cikin harkokin cikin gidansu. Haka zalika su ma shuwagabannin wadannan kasashe sun jaddada cewa kasashensu za su ci gaba da zurfafa huldar arziki tsakaninsu da kasar Sin a fannonin ci gaban kasashensu da suka hada da abubuwan more rayuwa, da bunkasa tattalin arzikinsu, da aikin gona da horar da ma’aikata, da tsaro, da samar da allurar rigakafin cutar COVID-19.

Kamar dai yadda na lura, babban muhimmancin wannan ziyara a wannan shekara kamar yadda yake faruwa a kowace shekara, shi ne jerin takardu na yarjejeniyoyi na hadin gwiwa da aka rattaba ma hannu tsakanin wadannan kasashe da kasar Sin, tabbas za ta kuma kara dankon zumunta, da mutunta juna. Duk yawanci dai ababen dake rattaba ma hannu suna da nasaba da “ayyuka tara” na hadin gwiwar dandalin FOCAC da kuma na tsarin “ziri daya da hanya daya”.

Bayan alherin da wannan ziyara za ta kawo wa Afirka, ziyarar wani darasi ne ga wasu kasashe wadanda ke tsoma baki suna maganganu da neman sa cikas a dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. Akwai alamar wannan katsalandan ba zai samu tasiri ba saboda a halin da ake ciki yanzu kasar Sin tana da dangantaka da huldar diflomasiyya da kusan duk kasashen Afirka, kuma a kowace kasa a nahiyar Afirka akwai abin da kasar Sin ta yi na a zo a gani kamar irin su layin dogo, da gadoji, da tashar jiragen ruwa, da filayen jiragen sama, da madatsun ruwa, da kuma kokarin da Sin take yi na ganin nahiyar Afirka ta samu issasun alluran rigakafin cutar COVID-19. Hulda tsakanin kasashen namu dai tamkar hulda tsakanin ’yan uwa ce.

A wasu kalamai da Minista Wang Yi ya yi a Kenya, ya ce “nahiyar Afirka ba dandalin gasa ba ne tsakanin kasashe, Afirka wuri ne da ya zama dandalin hadin gwiwar kasa-da-kasa”. Ya ce, “idan akwai gasa, kamata ya yi ta zama ta gasar da ta fi taimakawa nahiyar”. Shi ma a nashi bayanin, shugaba Uhuru Kenyatta ya ce, “nahiyar Afirka ba ta bukatar lacca, abin da take bukata shi ne abokai na-gari, kuma Afirka ta riga ta samu aboki nagari a Sin.”

Wannan ziyara dai abin alfahari ne tsakanin kasar Sin da Afirka kuma muna fata za mu ci gaba da ganin nasarori da ci gaba a kasashen namu. (Lawal Sale)