logo

HAUSA

Gobara ta kashe mutane 19 a birnin New York

2022-01-10 10:23:12 CRI

Gobara ta kashe mutane 19 a birnin New York_fororder_哦哦

A kalla mutane 19, da suka hada da yara kanana tara ne suka mutu a wata mummunar gobara da ta faru a birnin New York na kasar Amurka a ranar Lahadi, magajin birnin New York, Eric Adams ya tabbatar da faruwar lamarin.

Eric ya godewa jami’an sashen kashe gobara na birnin New York (FDNY) sakamakon nasarar kashe gobarar, wacce ta barke a wani dogon beni mai dauke da gidajen kwana dake yankin 333 East 181st a kan titin Bronx.

A cewar magajin garin, an garzaya da mutane 32 zuwa asibiti domin ceto rayuwarsu. Bugu da kari, mutane tara suna cikin mummunan yanayi, kana wasu mutanen 22 sun samu kananan raunuka. Daya daga cikin ma’aikatan kashe gobarar shi ma an garzaya da shi zuwa asibiti.

Kwamishinan hukumar FDNY, Daniel Nigro, wanda ya ziyarci wajen tare da Adams, ya ce gobarar ta barke ne a beni hawa na 2 da na 3 na ginin. Kofar rukunin gidajen ta kasance a bude, inda hakan ya kara gudanuwar iska da hayaki cikin sauri cikin ginin mai hawa 19.

Nigro ya ce, wannan bakon al’amari ne da ba a saba gani ba a birnin. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Hukumar kashe gobarar za ta gudanar da cikakken bincike.(Ahmad)