logo

HAUSA

Beijing Olympic 2022: Hukumomin kasa da kasa sun gamsu da matakan kare lafiyar mahalarta gasa da Sin ta dauka

2022-01-10 17:36:55 CRI

Beijing Olympic 2022: Hukumomin kasa da kasa sun gamsu da matakan kare lafiyar mahalarta gasa da Sin ta dauka_fororder_0110-1

Yayin da ya rage kasa da wata guda a bude gasar babbar gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022, mahukunta kasa da kasa sun bayyana gamsuwarsu game da irin matakan da gwamnatin Beijing ta dauka don karbar bakuncin wasannin, har ma wasu na da ra’ayin cewa, tsauraran matakan rigakafin da Sin ta dauka za su ba da tabbaci na gudanar da wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing yadda ya kamata. Ko da a karshen makon da ya gabata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, daukar tsauraran matakai na rigakafi a jere, za su ba da tabbaci ga gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing yadda ya kamata. Wang Wenbin ya ce, a sakon taya murnar sabuwar shekara da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya bayyana aniyarsa na sadaukar da gasar Olympic ga daukacin duniya. Kazalika, a ranar farko ta sabuwar shekarar bana, shugaban na Sin ya ziyarci wuraren da ake shirin karbar bakuncin muhimmiyar gasar ta lokacin hunturu, da ajin gasar ta nakasassu, hakan na nuni da muhimmanci da Sin ke dorawa kan shirya gasar ta Olympic bisa alkawarin da ta riga ta dauka. Sannan kuma, kyakkyawan shirin da Sin ta yi domin gudanar da gasar ya nuna karfin gwiwar da kasar ke da shi na gudanar da gasar bisa cikakken tsaron lafiyar mahalartanta wasannin duk da irin kalubalolin annobar Covid-19 da ake fuskanta. Hakika, jerin gwanon matakan dakile cutar COVID-19 da Sin ta dauka a yayin gasar sun ja hankalin kasa da kasa. Misali, a karshen wannan mako, wani babban jami’in hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce, shirin da gwamnatin birnin Beijing ta yi don tabbatar da dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 a yayin gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022 suna da karfin gaske. Michael Ryan, daraktan sashen ayyukan gaggawa na hukumar WHO, ya yi nuna da cewa, hukumar tana aiki da kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa IOC domin samun shawarwarin kwararru game da yadda za a karbi bakuncin gasar lami lafiya. An jiyo Michael Ryan yana cewa, hukumomin kasar Sin sun dauki tsauraran matakai, kuma sun fitar da jerin littattafan ba da jagora daban daban game da batutuwan dake shafar yaki da annobar. Ya kara da cewa, yana da kwarin gwiwa bisa ga bayanan da ake da su cewa, matakan da kasar Sin take dauka kawo yanzu game da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022 suna da matukar tsauri kuma suna da matukar karfi, kuma a halin yanzu, babu wata karuwar barazanar yaduwar cutar. Dama da masu hikimar magana na cewa, “Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta”. (Ahmad Fagam)