logo

HAUSA

Sin ta bayyana goyon bayanta ga Kazakhstan a wannan muhimmin lokaci da take ciki

2022-01-10 15:42:26 CRI

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da mataimakin firaminista kuma ministan harkokin wajen kasar Kazakhstan Muktar Tleuberdi a yau Litinin, inda ya ce a matsayinta na abokiyar hadin gwiwar Kazakhstan na dindindin, a shirye Sin ta ke ta taimaka mata wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kawo karshen rikici, a wannan muhimmin lokacin dake da tasiri kan makomar kasar.

A cewar Tleuberdi, yau rana ce ta makoki a kasar. Kuma kiran da ya samu daga ministan harkokin wajen Sin, ya kara nuna goyon baya da ‘yan uwantakar dake tsakaninsu. Ya kuma yi bayanai game da yanayin da kasar ke ciki, yana mai cewa, an shawo kan rikicin, inda aka samu dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya ce Kazakhastan za ta tabbatar da tsaron hukumomin kasa da kasa da jami’ansu da jarin kasashen waje, tare da ci gaba da sauke nauyin dake wuyanta ta fuskar yarjejeniyoyin duniya.

A nasa bangaren, Wang Yi, ya ce a wannan rana da Kazakhstan ke zaman makoki, Sin na jinjinawa jami’an tsaron da suka mutu a fagen daga wajen shawo kan rikici da ta’addanci a kasar, inda kuma ya jajantawa iyalan mamatan da wadanda suka jikkata. (Fa’iza Mustapha)