logo

HAUSA

Sharhi:Afirka na bukatar aminai na gaske ne maimakon yi mata lacca

2022-01-09 21:29:09 CRI

Sharhi:Afirka na bukatar aminai na gaske ne maimakon yi mata lacca_fororder_f7246b600c33874473ec6d86dba468f0d62aa050

“Kenya-Afirka ba sa bukatar a yi musu lacca, a maimakon haka, muna bukatar aminai da ke son hadin gwiwa da mu don cimma burin da muka sanya a gaba. Yau ina so in bayyana wa shugaban kasar Sin da gwamnatin kasar da al’ummarta godiya……”

Daga ranar 4 zuwa 7 ga wata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kai ziyara kasashen Afirka uku, da suka hada da Eritrea, Kenya da kuma Comoros. A yayin ziyararsa a kasar Kenya, Wang Yi, ya halarci bikin kaddamar da tashar mai ta Kipevu(KOT) da kasar Sin ta gina, bisa gayyatar da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi masa. A gun bikin, shugaba Kenyatta ya nuna babban yabo kan yadda kasar Sin ke tallafawa Kenya don tabbatar da ganin ci gabanta, kuma a cewarsa Sin “aminai ne na gaskiya”, ya kuma bayyana godiyarsa ga kasar Sin.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Kenyatta ya ce, tsohuwar tashar mai ba ta iya biyan bukatun kasar ba yayin da tattalin arzikinta ke dada bunkasa, don haka take bukatar wata tashar sabuwa. “Da muke neman gina ta, to, ga kasar Sin tana nan, a shirye take ta hada gwiwa da mu, lalle abu ne da muke kira aminai na gaske. Ba ma bukatar a yi mana lacca, a maimakon haka, muna bukatar abokan hadin gwiwa da za su iya biyan bukatunmu.”

An ce, aikin ginin tashar KOT na tattare da manyan fasahohi da wahalar aiwatarwa, kuma wani aiki ne mai matukar inganci, da ya dace da yanayin kare albarkatun ruwa, zai kuma samar da guraben ayyukan yi a yankin, tare da damammakin kasuwanci.

Sharhi:Afirka na bukatar aminai na gaske ne maimakon yi mata lacca_fororder_20220107205456864

A hakika, tashar KOT ta kasance wani misali ne kawai na hadin gwiwar Sin da Kenya da ma hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta fannin raya manyan ayyukan more rayuwa. Ya zuwa yanzu, Sin da Afirka sun hada hannu wajen gina sama da kilomita 10,000 na layin dogo, da titunan mota masu tsayin kusan kilomita 100,000, da gadoji kusan 1,000, da tashoshin ruwa kusan 100, tare da tarin asibitoci da makarantu.

Sai dai hakan ba abu ne da Amurka da sauran kasashen yamma suke son gani ba, wadanda suke kokarin yayata kalamai na wai “barazana daga kasar Sin” da “sabon mulkin mallaka”, a yunkurin kawo cikas ga hadin gwiwar sassan biyu. Idan ba a manta ba, a yayin ziyarar sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken a kasar Nijeriya a watan Nuwamban bara, ya zargi kasar Sin da haifar da matsalar basussuka ga kasashen Afirka. Amma nan da nan furucinsa ya jawo suka daga wajen takwaransa na Nijeriya Mr. Geoffrey Onyeama, wanda ya ce, basussukan da Nijeriya ta ci ba su da yawa, wadanda Nijeriya ke iya biya ne, kuma dalilin da ya sa aka zabi kamfanonin kasar Sin wajen bunkasa manyan ababen more rayuwa a kasar shi ne, kamfanonin sun kware, kana suna samar da farashi mai rahusa. Ya jaddada cewa, “ciniki mafi kyau muke magana, a maimakon zancen wannan kasa ko waccan kasa.”

Sharhi:Afirka na bukatar aminai na gaske ne maimakon yi mata lacca_fororder_rBABDGGbirKAANCAAAAAAAAAAAA93.640x427

A zahiri dai, al’ummar Afirka sun san ko hadin gwiwarsu da kasar Sin ya amfane su ko a’a. Kasashen Afirka ba sa bukatar a yi musu lacca, a maimakon haka, suna bukatar aminai da ke son hadin gwiwa da su don cimma burin da suka sanya a gaba

Kasar Sin har kullum tana kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara mai da muhimmanci a kan Afirka, kuma kullum tana maraba da kasa da kasa musamman ma kasashe masu ci gaba da su sanya hannu a aikin tabbatar da ci gaban kasashen Afirka. Daidai kamar yadda minista Wang Yi ya bayyana a yayin wannan ziyararsa, “Ya dace nahiyar Afirka, ta zamo babban dandali na hadin gwiwar kasa da kasa, ba wai wani fage na takarar manyan kasashe ba. Idan akwai wata gasa, kamata ya yi ta zama ta gano kasar da ta fi tallafawa nahiyar, wanda ta baiwa nahiyar agaji mafi yawa, ko wadda ta fi gudanar da ayyuka domin al’ummun nahiyar.”

Ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai nahiyar Afirka a wannan karo ta kasance al’adar da kasar Sin ta kiyaye cikin shekaru 32 da suka gabata, baya ga haka kuma, ziyara ce da ministan ya kai Afirka bayan taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a bara. Bana ne shekara ta farko da aiwatar da muhimman ayyukan hadin gwiwa guda tara da aka sanar a gun taron, kuma tabbatar da sakamakon taron na daga cikin manyan manufofin da ministan harkokin wajen kasar Sin ke neman cimmawa a wannan ziyarar tasa. A farkon sabuwar shekara, an soma hadin gwiwar Sin da Afirka yadda ya kamata, don haka muna sa ran hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu, zai ci gaba da samun bunkasuwa mai kyau a nan gaba. (Lubabatu)