logo

HAUSA

‘Yan sama jannati na Shenzhou-13 sun kammala gwajin haduwar tashar sararin samaniya da kumbon dakon kaya

2022-01-08 20:32:17 CRI

‘Yan sama jannati na Shenzhou-13 sun kammala gwajin haduwar tashar sararin samaniya da kumbon dakon kaya_fororder_1128243719_16416067813001n

Hukumar sararin samaniya ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, ‘yan sama jannati na Shenzhou-13 dake tashar sararin samaniyar kasar, sun kammala gwajin haduwar tashar sararin samaniya ta kasar da kumbon dakon kaya na Tianzhou-2.

Sarrafa kumbon da ‘yan sama jannatin suka yi, na zaman madadi ga aikin haduwar kumbon mara matuki da zai iya gudana kai tsaye. Gwajin shi ne karon farko da ‘yan sama jannatin kasar suka yi bisa amfani da na’urar sarrafa kumbun dakon kaya daga nesa, kuma karon farko da tashar ta gudanar da wannan aiki. (Fa’iza Mustapha)