logo

HAUSA

Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin a nahiyar Afirka za ta gaggauta aiwatar da sakamakon da aka samu a dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka.

2022-01-08 20:25:28 cri

Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin a nahiyar Afirka za ta gaggauta aiwatar da sakamakon da aka samu a dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka._fororder_0c88af3e-8056-4e4c-acd1-51c4173a7590

Daga ranar 4 zuwa 7 ga wata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya ziyarci kasashen Afirka uku, wato Eritrea, Kenya da Comoros. Ziyarar farko da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai nahiyar Afirka a farkon wannan shekara, ba wai al'adar diflomasiyya ta kasar Sin ce ta shekaru 32 kadai ba, har ma ita ce ziyarar aiki karo na biyu da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai nahiyar Afirka bayan kammala taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar a shekarar da ta gabata.

Gaggauta aiwatar da sakamakon da aka cimma a dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na daya daga cikin muradu uku na ziyarar mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi. Misali, an rattaba hannu kan wasu jerin takardun hadin gwiwa da kasar Kenya a yayin ziyarar, wanda daya ne daga cikin "ayyuka tara" na hadin gwiwar dandalin FOCAC. Wakiliyar musamman ta gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka Xu Jinghu ta bayyana cewa, a cikin shekaru 20 da suka gabata tun bayan kafa dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa wajen gina layin dogo, da hanyoyin mota, da gadoji da tashoshin jiragen ruwa da dai sauransu a nahiyar Afirka, wadanda suka ba da babbar gudummawa wajen inganta ababen more rayuwa a nahiyar.

Xu Jinghu ta kara da cewa, 2022 ita ce shekarar farko ta fara aiwatar da "ayyuka tara". A farkon sabuwar shekara, an soma hadin gwiwar Sin da Afirka yadda ya kamata. Ana sa ran cewa, hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu, za ta ci gaba da samun bunkasuwa mai kyau a nan gaba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)