logo

HAUSA

Shugaban hukumar CAF ya isa Kamaru domin kaddamar da gasar cin kofin Afirka

2022-01-08 16:07:27 CRI

Shugaban hukumar CAF ya isa Kamaru domin kaddamar da gasar cin kofin Afirka_fororder_gettyimages-994504746-594x594

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika (CAF) Patrice Motsepe, ya isa Douala, cibiyar kasuwanci ta kasar Kamaru a jiya Juma’a, gabanin fara wasanni gasar cin kofin Afrika da za a yi a kasar.

Patrice Motsepe, zai jagoranci bikin bude gasar tare da shugaban kasar Kamaru Paul Biya, a filin wasa na Olembe dake Yaounde, babban birnin kasar.

Za a fara wasan ne da Kamaru mai masaukin baki, inda za ta kara da Burkina Faso, da ‘yan wasanta suka isa Kamarun tun a farkon wannan mako.

Kungiyoyi 20 daga cikin 24 da za su fafata a gasar, sun riga sun isa kasar ta yammacin Afrika.

A jiya Juma’a ne ministan lafiya na kasar ta Kamaru, Manoada Malachie, ya ce ana matukar bukatar alluran riga kafin COVID-19 a kasar, gabanin kaddamar da gasar a gobe Lahadi.

A cewarsa, gwamnati ta samar da wani dandali da zai ba jama’a damar yin registar karbar riga kafin da ma yin gwaji cikin sauri. Ya ce wadanda suka yi riga kafi da gwaji ne kadai za a ba su shaidar da za ta ba su damar shiga filin wasan. (Fa’iza Mustapha)