logo

HAUSA

Wane ne ke kawo "barazana" a yankin Asiya da Pacific?

2022-01-08 21:28:35 cri

Wane ne ke kawo "barazana" a yankin Asiya da Pacific?_fororder_微信图片_20220108204117

Jiya Jumma’a, ministocin harkokin wajen Amurka da na Japan sun yi wani taro ta yanar gizo, tare kuma da fitar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka sake yin tsokaci kan batutuwan da suka shafi kasar Sin, tare da wuce gona da iri kan abin da ake kira "barazana daga kasar Sin", bangarorin biyu sun kuma rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro. Sai dai kwana guda kafin hakan, kasashen Japan da Australia ma sun nuna yatsa kan harkokin cikin gidan kasar Sin a yayin shawarwarin da aka gudanar tsakaninsu, tare da sanya hannu kan wata yarjejeniya game da hadin gwiwar tsaro.

A farkon sabuwar shekara, lokacin da al'ummar yankin Asiya da tekun Pasifik ke fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, wadannan shawarwari guda biyu da suka cika da tunanin yakin cacar baka, kalubale ne ga zaman lafiya da zaman karko a yankin. Irin matakin da Amurka da kawayenta irin su Japan da Australia ke dauka, shi ne ainihin barazana ga "rashin zaman lafiya" a yankin Asiya da tekun Pasifik.

A matsayinsa na yanki mafi fa'ida da kuma samun makoma mai kyau a nan gaba a duniya, samun ci gaba cikin lumana shi ne burin jama'ar yankin Asiya da tekun Pasifik baki daya. Sakamakon aiwatar da yarjejeniyar RCEP, yanayin hadin kai a yankin Asiya da tekun Pasifik ya zama abin da ba za a iya juyawa ba, kuma riko da "ainihin ra’ayin bangarori da dama" ya fi samun karbuwa a yankin. Amurka da Japan da kuma Australia sun hadu don shiga cikin "karamar da'ira" don yaki da wasu kasashe, hakan ba zai samu amincewa ba, kuma ko shakka babu burinsu zai bi ruwa. (Mai fassara: Bilkisu)