logo

HAUSA

Shugaban kasar Kenya ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin

2022-01-07 10:01:49 CRI

Shugaban kasar Kenya ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin_fororder_220107-A1-Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, a ranar Alhamis ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, bisa goron gayyatar da aka ba shi zuwa kasar ta Afrika.

Kenyatta ya bukaci Wang ya isar da sakon gaisuwarsa ga shugaba Xi Jinping. Kenyatta ya ce, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya kai zuwa kasar Kenya a farkon shekara ya kara nuna muhimmiyar dangantaka mai karfi dake tsakanin Kenya da Sin.

Kenyatta ya ce, hadin gwiwar dake tsakanin Kenya da Sin ya shafi goyon baya na hakika tsakanin abokan hulda na gaskiya. Ya ce dalilin da ya sa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Kenya da Sin ke kara kusanci da juna shi ne, saboda kasashen biyu suna mutunta junansu kuma suna daukar junansu a matsayin makusanta.

Wang ya fara ne da isar da sakon gaisuwar fatan alheri ta shugaba Xi zuwa ga shugaba Kenyatta, kana ya taya kasar Kenya murnar cigaban da take samu cikin sauri karkashin shugabancin Kenyatta.

A cewar Wang, ziyarar za ta isar da muhimman sakonni guda uku. Na farko, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen yin hadin gwiwa da Afrika don yaki da cutar numfashi ta COVID-19 tare da goyon bayan juna har a samu cimma nasarar kawar da cutar.

Na biyu, kasar Sin a shirye take ta karfafa hadin gwiwarta da kasar Kenya daga dukkan fannoni domin taimakawa Kenya wajen samun damar bunkasa ci gaban kanta da bunkasa fannin masana’antu.

Na uku, kasar Sin a shirye take ta karfafa goyon baya da hadin gwiwa da kasar Kenya game da batutuwan dake shafar kasa da kasa da hadin gwiwar bangarori daban daban, domin tabbatar da kiyaye muhimman hakkokin kasashen biyu da kuma kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da kiyaye huldar kasa da kasa bisa gaskiya da adalci. (Ahmad Fagam)