logo

HAUSA

Wang Yi: Tarihi da shaidu na zahiri za su fayyace su waye aminan Afirka na gaskiya

2022-01-07 20:54:50 CRI

Wang Yi: Tarihi da shaidu na zahiri za su fayyace su waye aminan Afirka na gaskiya_fororder_W020220107376942272400

Babban dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce tarihi da shaidu na zahiri ne za su fayyace su waye aminan nahiyar Afirka na gaskiya. Wang Yi, ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da tashar mai ta Kipevu(KOT) dake kasar Kenya da kasar Sin ta gina, bisa gayyatar da shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya yi masa, a gefen ziyarar aiki da yake yi a kasar.

Wang ya taya Kenya murnar kammala karin wani muhimmin aikin raya kasa, karkashin jagorancin Kenyatta, yana mai cewa tashar ta KOT, za ta amfani Kenya da ma shiyyar ta.

Minista Wang, ya ce aikin ginin tashar KOT na tattare da manyan fasahohi da wahalar aiwatarwa, kuma wani aiki ne mai matukar inganci, da ya dace da yanayin kare albarkatun ruwa, zai kuma samar da guraben ayyukan yi a yankin, tare da damammakin kasuwanci.

Ya kara da cewa, dukkanin wadannan, shaidu ne dake nuna yadda hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya ke ingiza ci gaba, da wanzar da kawancen al’ummun sassan biyu, bisa manufofin da shugaban Sin Xi Jinping da jagororin Afirka suka tsara.

Kaza lika, Wang ya ce batun zamanantar da harkoki, ba kalaman baka ba ne, aiki ne ke tabbatar da su, kuma Sin da Afirka sun hada hannu wajen gina sama da kilomita 10,000 na layin dogo, da titunan mota masu tsayin kusan kilomita 100,000, da gadoji kusan 1,000, da tashoshin ruwa kusan 100, tare da tarin asibitoci da makarantu.

Kari kan hakan, minista Wang, kowace kasa na da ikon tabbatar da ci gabanta, kuma ko wace kasa ta samu damar cimma burikanta yadda ya kamata.

Ya ce ya dace nahiyar Afirka, ta zamo babban dandali na hadin gwiwar kasa da kasa, ba wai wani fage na takarar manyan kasashe ba. Ya ce "Idan akwai wata gasa, kamata ya yi ta zama ta gano kasar da ta fi tallafawa nahiyar, wanda ta baiwa nahiyar agaji mafi yawa, ko wadda ta fi gudanar da ayyuka domin al’ummun nahiyar.   (Saminu)