logo

HAUSA

Tsauraran matakan rigakafi, za su ba da tabbaci ga gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing yadda ya kamata bisa lokacin da aka tsara

2022-01-07 20:05:30 cri

Tsauraran matakan rigakafi, za su ba da tabbaci ga gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing yadda ya kamata bisa lokacin da aka tsara_fororder_c8ea15ce36d3d539aed04e0227fd5859372ab081

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Jumma’a cewa, daukar tsauraran matakai na rigakafi a jere, zai ba da tabbaci ga gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing yadda ya kamata, bisa lokacin da aka tsara.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 6 ga wata, babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO), mai kula da ayyukan gaggawa Michael Ryan, ya bayyana cewa, matakan rigakafin annobar COVID-19 na wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, na da tsauri da inganci. Ko da yake an samu bullar annobar a kasar Sin a 'yan makonnin nan, amma idan aka yi la'akari da shirye-shiryen da kasar Sin ta yi wa mahalarta wasannin, WHO ta yi imanin cewa, babu wani karin hadarin bazuwar annobar, a yayin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing. (Bilkisu Xin)