Kwalliya ta biya kudin sabulu a kokarin da kasar Sin ke yi na inganta muhalli
2022-01-07 22:25:33 CRI
“A tarihin kasar Sin, alummun Sinawa suna sa ran kiyaye Rawayen kogin, a cikin yan shekarun da suka gabata, na ziyarci jihohi tara da kogin ya ratsa, ko Rawayen kogi, ko kogin Yangtse, wadanda aka mayar da su a matsayin mahaifiyar alummun Sinawa, ko tafkin Qinghai, ko kogin Yarlung Zangbo, ko babban aikin sauya hanyar ruwa daga kudu zuwa arewa, ko gandun daji na Saihanba, ko kaurar giwaye daga kudu zuwa arewa a lardin Yunnan, da komawa inda suka fito, ko kaurar gadar jihar Tibet, duk wadannan sun nuna cewa, idan bil adama ya yi kokarin kiyaye muhalli, to tabbas za a cimma burin da aka sanya gaba."
Kamar yadda aka saba, a jajebirin sabuwar shekara ta 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, don isar da gaisuwar sabuwar shekara ga alummun cikin gida da na ketare, inda kuma ya waiwayi alamuran da suka wakana cikin shekarar 2021 da aka ga karshenta,ciki har da ci gaban da kasar ta samu ta fannin kiyaye muhalli.
A hakika, a shekarar da ta gabata, raayin kiyaye muhalli ya kara samun gindin zama a zukatan jamaar kasar Sin, kuma an cimma sabbin nasarori wajen kiyaye da inganta muhalli a kasar, matakin da ya samar da himma da karfi ga aikin inganta muhalli a fadin duniya.
A kasance tare da mu cikin shirin, don jin karin haske.(Lubabatu)