logo

HAUSA

Shekara Daya Bayan Tarzomar Da Aka Yi A Ginin Capitol, "Dimokradiyyar Amurka" Ta Kara Yin fama da Rashin Lafiya

2022-01-07 21:47:17 cri

Shekara Daya Bayan Tarzomar Da Aka Yi A Ginin Capitol, "Dimokradiyyar Amurka" Ta Kara Yin fama da Rashin Lafiya_fororder_微信图片_20220107204439

Ranar 6 ga watan Janairu, ita ce ranar cika shekara daya da tarzoma ta barke a ginin Capitol na Amurka. A cikin shekarar da ta gabata, Amurka ta kasance cikin rarrabuwar kawuna, kuma duniya ta ga cewa: “Dimokradiyyar Amurka” ta kara yin rashin lafiya!

Wani bincike na baya-bayan nan da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya gudanar ya nuna cewa, kashi 30% na ‘yan jam’iyyar Republican, sun dauki lamarin ginin Capitol “Ba tashin hankali ba”; yayin da kashi 90% na ‘yan jam’iyyar Democrat ke ganin abin da ya faru a ginin Capitol “Tashin hankali ne” ko “mummunan tashin hankali.” Ra’ayin ’yan siyasar kan yadda lamarin ya faru, ya zama shaida ta mubaya’arsu ga jam’iyyunsu. Wani bala’i ya zama makamin jam’iyyu da gwamnati, wanda ko shakka babu, babban abin kunya ne ga “dimokradiyyar Amurka.”

A sa'i daya kuma, rarrabuwar kawuna, da tarzomar da aka yi a ginin Capitol, ta kara tsananta tsarin "siyasar neman goyon bayan masu ruwa da tsaki ta Amurka”. A cikin shekarar da ta gabata, yiwa harkokin 'yan sanda kwaskwarima, da matakan sarrafa bindigogi, da tsare-tsaren kashe kudi a fannin tattalin arziki, da sauran ayyukan da suka shafi rayuwar jama'a sun ci gaba da tsayawa a kai a kai, kuma tsarin tafiyar da zamantakewar al'umma a Amurka ya tsaya cik. Wannan kuma ya nuna cewa, tsarin dimokuradiyya irin na “mutum daya da kuri'a daya” da 'yan siyasar Amurka ke goyon baya, wani tsari ne kawai da ba zai iya kare muradun masu kada kuri'a kwata-kwata ba.

Dimokuradiyya ba abu ne da ake amfani da ita wajen yin ado ba, ana amfani da ita ne don magance matsalolin da jama’a ke bukata a warware. Ya kamata wadancan ’yan siyasar Amurka, su yi watsi da son kai da neman mallake wasu, su kuma gaggauta ba da jinya ga “Dimokradiyyar Amurka”. (Mai fassara: Bilkisu Xin)