logo

HAUSA

Shugaban kasar Comoros ya gana da Wang Yi

2022-01-07 21:40:39 cri

Shugaban kasar Comoros ya gana da Wang Yi_fororder_W020220107833528599943

Jiya Alhamis a birnin Moroni, shugaban kasar Comoros Azali Assoumani, ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, wanda aka gayyata zuwa Comoros.

Azali Assoumani ya bayyana cewa, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai kasar Comoros, bisa halin da ake ciki na yaki da annobar COVID-19, ta nuna cewa, yana mai da hankali sosai kan dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Comoros da Sin, da kuma zumunci ga jama'ar kasar.

Ya ce kasar Sin tana kan muhimmin matsayi a zuciyar ‘yan Comoros. Kuma a madadin gwamnati da jama'ar kasarsa, ya kara jaddada cewa, Comoros za ta ci gaba da kasancewa tare da kasar Sin, ta kuma yi imanin Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, da ba za a iya balle shi ba, kuma ko shakka babu za a samu dinkewar kasar Sin.

Baya ga haka, Azali Assoumani ya godewa kasar Sin, bisa taimakon da take baiwa kasar Comoros a fannin tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, ya kuma yi tsokaci kan kokarin da kasar Sin ke yi na taimakawa Comoros, wajen yaki da annobar COVID-19 da cutar zazzabin cizon sauro. Kana ya yaba da muhimmiyar rawar da kamfanonin kasar Sin suke takawa, wajen gina manyan kayayyakin more rayuwa, da inganta rayuwar jama'a, yana kuma fatan samun karin goyon baya daga kasar Sin, wajen ciyar da "Shirin raya kasa nan da 2030” gaba.

A nasa bangaren, Wang Yi ya mika godiyarsa ga kasar Comoros, bisa goyon bayan da ta baiwa kasar Sin kan sahihin matsayi da ta dauka, ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da Comoros, a wasu batutuwan da suka shafi mulkin kan kasa, da cikakken yankin kasa, da kuma mutuncin al’umma.

Haka zalika, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son taimakawa Comoros wajen cimma muradu uku. Da farko cimma burin yin alluran rigakafi ga duk al’ummar kasar a cikin shekarar nan. Kasar Sin za ta goyi bayan Comoros wajen yaki da annobar COVID-19, za ta samar da alluran rigakafi kamar yadda Comoros ke bukata, har sai ta shawo kan annobar baki daya. Na biyu kuma, akwai batun kawar da zazzabin cizon sauro gaba daya nan da shekarar 2025. Na uku, Sin za ta goyi bayan dabarun ci gaban kasar, karkashin "Shirin raya kasa nan da shekarar 2030”.