logo

HAUSA

Me ya sa 'yan siyasar Amurka suka firgita sakamakon bude shago da Tesla ya yi a Xinjiang?

2022-01-06 20:21:36 cri

Me ya sa 'yan siyasar Amurka suka firgita sakamakon bude shago da Tesla ya yi a Xinjiang?_fororder_微信图片_20220106172118

Sakamakon bude wani shago a jihar Xinjiang, 'yan siyasar kasar Amurka sun sha zargin kamfanin motoci na Tesla na kasar. Kakakin Fadar White House Jen Psaki, ta tsoratar da kamfanin Tesla da cewa, "zai fuskanci babban hadari a fannonin doka, sunan sa, da kuma fannin abokan ciniki."

A matsayinsa na wanda ya shahara a duniya a fannin kera motoci masu amfani da wutar lantarki, me ya sa bude shagon da Tesla ya yi a jihar Xinjiang ya jawo irin wannan martani daga 'yan siyasar Amurka? Amsar ita ce, bude shagon Tesla a jihar ya sake tabbatar da cewa, abin da ake kira wai “dokar tilasta aiki ta Uygur” da Amurka ta tsara, tana cike da jita-jita!

Ga kamfanoni, yanayin kasuwanci mai kyau shi ne tushe na samun ci gaba. A cikin rubu'i uku na farkon shekarar 2021, yawan GDPn Xinjiang ya karu da kashi 8.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci a shekarar da ta gabaci hakan. Kaza lika daga shekarar 2014 zuwa ta 2020, yawan ma'aikatan jihar Xinjiang ya karu, daga kimanin miliyan 11.35 zuwa miliyan 13.56, adadin da ya karu da kashi 19.4 bisa dari. Ta yaya irin wannan yanki mai bunkasa ba zai burge kamfanoni da yawa daga kasashen waje ba?

A yau shekara daya da ta wuce, tarzoma ta barke a ginin Capitol na Amurka. Wani binciken jin ra'ayin jama'a da aka gudanar kwanan nan a kasar, ya nuna cewa, kashi 64 cikin 100 na masu ba da amsa sun yi imanin cewa, dimokuradiyyar Amurka "tana cikin rikici, kuma tana fuskantar hadarin gazawa." Wani abin da ya kara ba wa al'ummar Amurka bakin ciki shi ne, a farkon sabuwar shekarar nan, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar ya zarce miliyan 1 a rana guda, lamarin da ya karya matsayin adadin masu harbuwa da cutar a duniya.

"Dimokradiyyar Amurka" tana cike da matsaloli, kuma da kyar ake iya kare babban hakkin rayuwa na jama'ar kasar, bisa wannan halin da ake ciki, har yanzu 'yan siyasar Amurka suna nuna "damuwa" game da abin da ake kira wai "hakkin dan adam" a jihar Xinjiang mai nisa, wannan mataki ne na munafunci, kuma bisa ma’auni iri biyu!

(Mai fassara: Bilkisu Xin)